Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A farkon jawabinsa, Hujjatul Islam Sheikh Naim Qassem, Sakatare Janar na Hizbullah na Lebanon, ya ce: Ina taya Musulmai murna na shiga watan Sha'aban, watan Manzon Allah da kuma watan haihuwar Imamai As.
Ya ce: Imam Khamenei shine Shugaban da ke da nauyin jagoranci a lokacin ɓoyuwar Imam Mahdi (a.s.) kuma shine Mataimakin Imami Mai Adalci. Hizbullah ta yi imani da jagorancin Wilayatul Faiqh kuma tana da alaƙa da shi bangaren tunani da imani.
Babban Sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon ya ce: Yayin da Trump ya yi barazana ga Imam Khamenei, a zahiri yana barazana ne ga dubban miliyoyin masoyansa. Muna daukar wannan barazanar a matsayin barazana a kanmu kuma za mu dauki duk wani mataki da ya dace". Ya ce: "Wajibi ne mu fuskanci wannan barazanar gaba daya cikin shiri, domin duk wata cutarwa da zata samu Imam Khamenei, saboda yawan magoya bayansa da Jagorancinsa, yana a matsayin haifar da rashin zaman lafiya a yankin da kuma duniya baki daya.
Ba za mu iya yin shiru ba wajen fuskanci barazanar Trump ko wasu a kan Imam Khamenei, kuma za mu fuskanci barazanar da dukkan matakai da hanyoyi".
Sheikh Naim Qassem ya ce: "Amurka ta kaddamar da yakin shekaru takwas a kan Iran, ta yi amfani da dukkan nau'ikan makamai, ta kashe miliyoyin kudi don kifar da Iran, kuma ta gaza. Tun lokacin da aka kafa Jamhuriyar Musulunci a Iran a shekarar 1979, Amurka ta fara fuskanci hakan saboda ba za ta iya jure wa samuwar kasa mai 'yanci da cin gashin kanta ba wacce ke aiki a matsayin tushe madogara ga Musulmai da wadanda aka zalunta a duniya".
Ya kara da cewa: Kafa Jamhuriyar Musulunci da nasararta shi ne babban barazana ga Amurka da Isra'ila. Iran ta yi tsayin daka a yakin kwanaki 12, kuma a karkashin jagorancin Imam Khamenei, ta sami damar dakile shirin Amurka da Isra'ila. Makiya sun so su kifar da Iran daga cikin gida ta hanyar tattalin arziki, don haka suka kutsa kai da masu yi wa Iran zagon kasa wadanda suka kai hari ga jami'an tsaro da mutane suka kuma kona masallatai, motoci da cibiyoyin kasar.
Sakataren Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon ya jaddada cewa: Samar da Zaman lafiya da karfin zalunci yana nufin mulkin zalunci da mulkin mallaka da karfi, kuma kisan kare dangi da "Isra'ila" ke yi a Gaza yana nufin barna da aikata laifuka tare da hadin gwiwar kasashen yamma.
Ina gaishe da Jamhuriyar Musulunci kuma ina gaya wa mutanen Iran: Kuna da mutunci. Muna tare da ku kuma kuna tare da mu.
Kada ku yi mana barazana da mutuwa, domin mutuwa ba a hannunku ta ke ba, sai dai tana hannun Allah Madaukakin Sarki.
Amma daukaka da mutunci suna hannunmu kuma ba za mu yi watsi da su ba, domin wannan yana nuna nauyin da ya hau kanmu.
Shekh Naeem Qassem ya yi gargadin cewa: "Ba za mu kasance ‘yan kallo ba ga duk wani hari da za’a kai wa Iran".
Your Comment